Wednesday, 6 June 2018

LABARI DA DUMI-DUMINSA: YANZU HAKA YAN TA'ADDA SUN YIWA KAUYEN NA-WAJE, KAWANYA. Daga Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

LABARI DA DUMI-DUMINSA RASHIN TSARO: YANZU HAKA YAN TA'ADDA SUN YIWA KAUYEN NA-WAJE, KAWANYA.

Yanzu haka, 'Yan ta'adda sun Mamaye kauyen Na-waje, kasa da kilo mita 20 tsakanin garin da garin Mada a karamar Hukumar Gusau.

'yan ta'addan dauke da miyagun makamai sun yiwa al'ummar kauyen suna cigaba da bude wuta a kan mai uwa da Wabi. Al'ummar yankin sun tabbatar muna da cewa kwanakin baya, 'yan ta'addar sun Mamaye kauyen ne, bayan sun dauke wata mata, Mai ciki sun nemi kudin fansa miliyan uku, daga danginta. Amma ba a samu hada masu  kudin ba.

Kusan dai Dukkanin kauyukkan da ke yankin yanzu haka suna, cigaba da gudun hijira, a garin Mada da kuma garin 'Yandoto.

No comments:

Post a Comment

An yanke hukuncin kisa Akan mutane buyer; Ko me dalili?

Kotu ta yanke hukuncin kisa Akan was mutane biyar a dalilin kashe wani makiyayi da sukayi.  Abin ya faru ne a kauyen Kadamun da ke karamar h...