Thursday, 7 June 2018

ABUNDA EFCC TA YIWA MUKTAR LAMARAN YERO! YA YI DAIDAI: Inji Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu

ABUNDA EFCC TA YIWA
MUKTAR LAMARAN YERO!
YA YI DAIDAI DOMIN BA FIN
SAURAN TAKWARORINSA YA
YI BA!
Ni ba lauya ba ne, kuma ba Ni da ilimi Akan aikin lauya da
ma Shari'ar baki daya balantana in ce, an keta haddin
Tsohon Gwamnan Jahar Kaduna Muktar Lamaran Yero. Na
watsa shi a duniya tare da allon da ke nuna cewa ana
ZARGINSA da ya karbi hanci da rashawa. Duk da ba
tabbatar masa da laifinsa ba.
Sai dai ni a matsayina na Dan kasa, zan iya tofa albarkacin
bakina, kamar yadda na ke da damar haka a duk wani Abu
da Shari'ar ba ta katange ni gare shi ba.
Ya kamata mu yi nazari mai kyau!
Kusan Duk ofishin 'yan sandar jahar da ka leka a kasar nan
za ka tarar da hotonan mutane da aka zarginsu da aikata
wata aika-aikar har suka tafi hannun 'yan SANDAR!
Duk A lokacin da su ke gunsu ba masu laifi ba NE, Sai kotu
ta tabbatar masu da laifin amma hakan bai hana a dauki
hotonsu da kayan da ake zargin sun sata ko matara Kama
da haka, za a Sanya hotonansu duniya na cigaba da
kallonsu . Wannan kenan!
Duk wani mai cece-ku-ce Akan wannan hoton ina ganin
akwai daya a cikin wadannan a tare da shi.
Ko dai ya San Gaskiya Sak! Amma ya rike Karya,
Ko kuma ya kasance baida ilimi Akan yadda EFCC ke
gudanar da aikinta. Domin na tabbatar duk mai biyar shafin
facebook na wannan Hukumar zai ga yadda kusan kullum
su ke doro hotonan mutane da ake zargi da aikata ba daidai
ba. Wasu sun yi babban laifi wasu Kuma laifin bai taka-
kara-ya-karya ba. Amma zaka tarar sunansa baro-baro da
laifin da sunka yi ana yadawa duniya Kai tsaye, kamar
yadda aka yi kan Malam Lamaran Yero.
Wannan na nuna cewa Hukumar tana aiki kamar yadda yan
sanda ke a ofisoshinsu.
Amma dan dai son Kai irin namu mun yi caaa! Wai EFCC
TOZARCI ne da cin mutunci ta yi masa..
Sai dai abunda a ban sani ba, na San yana gwamna, yana
da rigar kariya ta musamman da zai gurfana a gaban kuliya
ba.
Yanzu Kuma ya sauka, ana tuhumarsa, Wanda hakan ma
NE, ya sa ya je ga EFCC, Anya kuwa an yiwa sauran
takwarorinsa adalci?
A cikin wannan rubutun na doro hotonan mutane da wasu
abinci ma ne su ke nema Dan talauci akwai wasu sunka tsiri
zamba, wannan Hukumar ta Dora hotunansu da abunda ake
tuhumarsu da yi
Haka zalika shi kansa LAMARAN ba Wai cewa aka yi an
tabbatar da laifinsa ba ne. Hoton tuhuma aka dauka kuma
kai mai kummar baki ka je ofisoshin 'yan sanda, kullum
haka suke wa wadanda ake tuhuma kafin kai su kotu. Sau
nawa kuma ake bayyana 'yan fashi da makami a gaban
'yan jarida, a baza hotunansu kuma har ma a yi magana da
su kafin a je kotu. Ko Evans mai garkuwa da mutane da aka
kama, an baza kolinsa ga yan jarida.
Dan haka in dai TOZARCI ne ko take hakkin Dan Adam NE,
to ba akansa aka soma ba, in Kuma har ya haramta a kudin
tsarin mulkin kasa, to Alhamdulillahi Talakan Najeriya da a
kullum ake walakantawa ya samu sa'ida. Domin an Fara
taba manya zai samu garkuwa kenan!
Dan haka ina amfani da wannan damar in yi roki rokarwa
shi lamaran Yero mafita.
Allah in wannan bawa naka na da Sanya hannu a wawurar
kudin talakawan Najeriya ka baiwa jami'an EFCC damar
gano badakalar tare da hukunta shi daidai laifinsa!
Allah in Kuma bai da sa hannu Allah ya yi masa mafita da
sauran makaraban da aka Kama su da shi.
Ya Allah ka Kare mu Daga fuskantar TOZARCI na duniya
uwa uba na kiyama. Allah ka sa mu karshe mai kyau.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

No comments:

Post a Comment

An yanke hukuncin kisa Akan mutane buyer; Ko me dalili?

Kotu ta yanke hukuncin kisa Akan was mutane biyar a dalilin kashe wani makiyayi da sukayi.  Abin ya faru ne a kauyen Kadamun da ke karamar h...