RASHIN TSARO: 'YAN GUDUN HIJIRA, SUN MAMAYE GARIN MADA.
Daruruwan 'yan gudun hijira Maza da mata yara Da tsofaffi ne, suka tserikke daga kauyukkansu da ke makwabtaka da garin Mada. Kauyukkan da suka hada da; Wonaka, Mai jiro, Hura girke, Dunkulawa sun tserikke ne, daga Kayukkansu domin tsira da rayukkan. Ganin yadda 'yan ta'adda su ke daukar rayukkansu kullum.
Yanzu haka Akwai sama da 'yan gudun hijira 300 da sun Fara baro kauyukkansu tun ranar Lahadi, inda su ke cigaba da zama a Makarantar Mada 1 Model primary school, Mada. Baya ga wadanda su ke a gidajen 'yan uwa da abukkan arziki da kuma garin 'yandoto.
Al'ummar karkara a Jahar Zamfara dai sun dade suna fuskantar kalubalen matsalar TSARO wanda ke dibar rayukkansu da dukiyoyinsu, a lungu da Sako na jahar.

No comments:
Post a Comment