Friday, 8 September 2017

Zan Jangoranci Raba Nigeria: Femi Fanni Kayode.

Tsohon Minitan sufuri na Najeriya, Femi Kayode, ya bayyana cewa zai jagoranci bangarewar kabilarsa ta Yarbawa domin bangarewar su daga najeriya. Femi Kayode ya kasance daya daga cikin mutane masu nuna tsananin kiyayyar su da wannan gwamnati ta shugaba Buhari. Hakan ne yasa yake nuna goyon bayan shi karara ga mai fafututar neman yankin Biafra, wato Namdi KANU.

To amma abinda yafi tada hankali da bada mamaki wa makusantar sa shine, shi namdi Kanun ya kasance mutum mai nuna tsananin kiyayyar su ga Kabilar Yarbawa amma Kayode bai daina bibiyar sa ba.

A cewar sa, Femi Kayode, idan har ba'a gyara tafir al'amura ba a Najeriya, to dole ne mu raba kasar Kuma ni zan jagoranci kabilar Yarbawa domin raba kasa.

Shin ko idan za'a raba kasan, dokacin masana, Manyan "yan siyasa, masu hanu da shuni da dattijan masu hangen nesa na cikin yarbawa kaf, zasu yadda Femi Kayode ya jagorance su?

No comments:

Post a Comment

An yanke hukuncin kisa Akan mutane buyer; Ko me dalili?

Kotu ta yanke hukuncin kisa Akan was mutane biyar a dalilin kashe wani makiyayi da sukayi.  Abin ya faru ne a kauyen Kadamun da ke karamar h...