AL'AMARIN KASAR BURMA
Marubuci : Dr Umar Abdulkaafiy
Babu laifi idan ka bayar da sakan 90 daga lokacin ka domin Kasan matsalar ((Burma)) da musulmi a cikin ta.
Kissar a takaice :
Kasa ce mai cin gashin kanta sunanta ARAKAN tana da musulmi miliyan uku, ta hanyar su sai musulunci ya fara yaduwa a Kasar da take makotaka da ita, sunanta BURMA wadda mafiya yawan mazaunanta mabiya addinin Buddah ne.
A shekara 1784 wato kimanin shekara dari biyu da talatin da suka wuce, sai mabiya addinin Buddah suka kullaci musulman ARAKAN dan haka suka yake su, suka kashe musulmi a cikinta, suka yi musu aika aika, suka hade Kasar ARAKAN da Kasar BURMA, suka canja sunanta izuwa (MYANMAR) ta dawo wani bangare na BURMA, sai musulmi suka dawo yan kadan bayan da sun Kasance kasa mai zaman kanta (adadinsu miliyan uku ko hudu) mafiya yawa sune mabiya addinin Buddah, adadinsu miliyan hamsin.
Sai musulmi suka samar da yan garuruwa masu cin gashin kan su, suna gudanar da rayuwar su a ciki, suna kasuwanci, acikin garuruwan akwai kungiyoyi da suke kula da masu wa'azin su da masallatansu.
Sai wadancan yan BURMA wato mabiya addinin Buddah suka rika kai farmaki a kan garuruwan musulmi; Saboda su kore su daga gidajensu.
A dan wani lokaci da bai jima da wucewa ba wasu kashe kashe masu ban tsoro sun afku, yayin da mabiya addinin Buddah marasa imani suka tare wata mota mai dauke da mutum goma na malamai masu kira zuwa ga addinin Allah, daga mahaddata Alqur'ani wadanda suke zagayawa garuruwan musulmi, suna haddatar da su Alqur'ani, kuma suna kiran su zuwa ga Allah, suna daura musu aure, tare da karantar da su sha'anin addinin su, wadannan mutane makiya Allah suka tare motar masu wa'azin nan, suka rika fito dasu suna dukansu duka mai fasa jiki, sannan suka rika wasa da wukake a jikinsu, sannan suka rika daure harshen su daya bayan daya sannan su cizgo shi tun daga makogwaronsa babu tausayi ba jin kai, duk wannan fa Saboda kullacin da suke musu akan suna kira zuwa ga addinin Allah, kuma suna koyawa mutane addini da Alqur'ani.
Sannan suka rika sukansu da wukake suna yanke hannayensu da kafafuwansu, har sai da suka mutu daya bayan daya🔪🔪..
Sai musulmi suka taso dan bada kariya ga malamansu kuma limaman masallatansu masu yi musu huduba.
Sai Mabiya addinin Buddah suka fuskanto su suka fara ƙone garuruwansu daya bayan daya, har sai da adadin gidajen da aka kona ya kai gida 2600 dubu biyu da dari shida, wadanda suka mutu suka mutu wadanda suka gudu suka gudu, mutum dubu 90 kuma suka yi sulale daga garuruwan ta hanyar kogi ko ta sarari, kuma yankan da kisan da ake wa musulmi har yanzu ana ci gaba da yi, kuma an kwace yanmatansu da yayansu mata da kuma matayensu, ga matsayin da zai kai zuwa ga kisa akan idon iyalansu, alhalin suma suna karkashin kaifin wukake🔪🔪..
Toh Meyasa bama kishinsu...?
Kowa ya tambayi kansa me zan iya yi musu..?
Abinda ya wajaba gareka a kansu a yanzu abu biyu ne:
Na daya...
Kayi musu addu'a...
Na biyu... Ka yada yada al'amarinsu dan mutane su sani... Wannan shi ne mafi raunin imani...
Idan ka gama karantawa.. Toh ka aikata abinda zuciyar ka ta raya maka, wannan fa idan zuciyar taka tana raye..?!!!
Allah ya isar mana Madalla da abin dogaro shi...
ku yada shi domin musulmi su san al'amarinsu
No comments:
Post a Comment