KUNGIYAR MATASAR AREWA TA JANYE WA’ADIN DA SUKA BAWA
IYAMURAI. KO ME YASA?
Kungiyar matasar arewa wacce akafi sani da “AREWA YOUTH
CONSULTATIVE FORUM” a turance, tace ta dakatar da wa’adin da suka bawa iyamurai
na barin yankin arewa kafin daya ga watan oktoban shekara 2017. Dama dai,
kungiyar ta umarci kabilar Ibo (iyamurai) da subar yankin arewan sabida
barazanar da shugaban mai fafutukar neman yankin Biafara, Namdi Kanu, yake yi
wa ‘yan arewa mazauna yankin Ibon.
Sanarwar janyewar dai ta biyo bayan tattaunawan da “yan
kungiyan sukayi ne a zangon baki na Transcorp hotel da ke birnin Abuja.
A wata majiya daga dakin taron yace janyewar korar ba ta dindindin
bane, bal, an dakatar ne na washin gadi kafin wasu lokuta a gani ko zasu ci
gaba da bada wani wa’adin.
No comments:
Post a Comment