A zantawar sa da wasu daga cikin jigogin Kungiyar Hausa/Fulani Youth Development and Orientation Forum (HAFYDOF) a ranar 11/July, 2017 kungiya mai fafutikar wayar da kai da kuma samar da cigaba ga Matasan Hausa/Fulani dama al'umma gabaki daya, ya bayyana cewa lallai su sun ci gajiyar Jagoranci na gari a zamanin su wurin su Sir Ahmadu Bello Sardauna da kuma Tafawa Balewa, inda ya tabbatar da cewa yau lamarin ba haka yake ba. Professor ya kara dacewa lallai matasa na bukatar hada kai don kawo cigaba wa Arewa.
kungiyar dai ta HAFYDOF na shirin gabatar da taron gangami ranar 27 zuwa 30 ga watan September don magance matsalar gurbataccen wakilci a Arewacin Nigeria.
No comments:
Post a Comment