Wata kungiya mai fafutukar kwato "yancin matasan arewa mai suna HAFYDOF, wato Hausa Fulani Youth Development And Orientation Forum, ta yunkuro don ceto halin da matasan arewa ke ciki. A gagarumin taron da sukayi a Kaduna, matasan sun gana da manya mutane masu kwatan wa arewa"yanci; irinsu Garfesa Ango Abdullahi. Tuni dai wadannan matasa suka fara koya wa mata da yara sana'o'i dabam dabam domin dogaro da kai. Wakilin mu na labarunduni.com ya sanar mana cewa sama da mutane (musamman mata) dari biyu ne suka ci moriyar wannan shiri na koyon sana'a na Kungiyar ta HAFYDOF a fadin kasan nan.
Bugu da kari, kungiyar bata tsaya nan ba ta bude makarantar koyon na'ura mai kwakwalwa (computer) a garin Jos yanda ta daukin nauyin koyar wa kyauta. Haka kuma suna da makarantar koyon harshen turanci da kwararrun malamai a cikin garin Jos.
A cewar sa, shugaban kungiyar ta kasa, Hon. Abdulaziz Tibibi, ana samun nasarar karbuwan kungiyar a fadin kasannan fiye da yadda ake tsammani. "Muna sa ran bude ofisoshim mu a duk fadin kasan nan bada dadewa ba", inji shugaba Tibibi.
No comments:
Post a Comment