Thursday, 13 July 2017

KO DA GASKE NE ZA'A BA KWANKWASO DAN MASANIN KANO?

A kwana kwanan nan ne maganganu suke ta bullowa cewa anji kishin kishin za'a bawa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankaso jim kadan da rasuwar shi dan masanin Kanon.

Amma daga wata Majiya Daga Masarautar Kano Ta Karyata batun Baiwa Kwankwaso Sarautar Danmasanin Kano Masarautar Kano ta musanta rahoto da ake yadawa a dandalin sada zumunta na  Facebook kamar haka;
         " Yayin Da Gwamnatin Jihar Kano Ke Kokarin Canja Sunan Makarantar Northwest  Zuwa Maitama Sule University, Ita Kuwa Masarautar Kano Na Shirye-Shiryen Nada *Rabi'u Kwankwanso*
Sarautar dan-Masanin Kano".
Jim kadan da samun wannan rahoton wata majiya ta tuntubu daya daga cikin hakiman Kano don tabbatarwa inda majiyar wacce ta nemi a sakaye sunanta, ta tabbatar mana da cewa "Uba da D'a ba sa zama a gaban Sarki daya a matsayin hakimai, sai dai shi Sarkin da 'Ya 'Yansa.  Kwankwaso mahaifinsa hakimi ne ba zai yiwu a ba shi hakimta ba sai dai in ya yi murabus, wannan labarun karya ne da makaryata suka saba kirkirowa kuma ai ba a bayar da sarauta ma sai da izinin gwamnatin jiha don haka mutane su kiyaye da yada jita-jita, in za'a bada sarauta ai masarauta ce zata sanar ba mutane ba tunda ba abu ne da ake yi a rufe ba." Inji majiyar. To amma masu iya magana sunce Idan kaga kare na sunsuna takalmi, to dauka zaiyi.

No comments:

Post a Comment

An yanke hukuncin kisa Akan mutane buyer; Ko me dalili?

Kotu ta yanke hukuncin kisa Akan was mutane biyar a dalilin kashe wani makiyayi da sukayi.  Abin ya faru ne a kauyen Kadamun da ke karamar h...