Kamfanin layin salula da aka fi sani da suna ETISALAT ta chanja sunanta daga sunan da aka fi saninta da shi zuwa 9Mobile. Hakan ya farune sabida masu hanun jari mafi tsoka na kamfanin sun janye hanunsu. Janyewar tasu ta faru ne aabida dumbun kudin da ake bin kamfanin da ya dara Dalar Amurka miliyan guda. Tuni masu kanfanin daga kasashen larabawa suka ce a daina amfani da sunan kamfanin su a nan Najeriya.
Hakan bai shafi sunan kamfanin ba a wasu kasashen da basu da matsala. A yanzu dai duk wanda ke da layin Etisalat din zai iya cigaba da aiki da shi amma netiwokin Etisalat ba, Sai da 9Mobile.
No comments:
Post a Comment