Hukumar "yan sandan Najeriya ta kama wajen kera muggan makamai a babban birnin tarayya Abuja.
A cewar Kwamishinan "yan sandan ta Abuja, yace an kama mutane uku wadanda ke da nasaba da kera makaman, da saida su ga masu saya. Mutane ukun da aka kama sun hada da: Philip John, mai kerawa; Onyegabueze da Joseph Bulus, masu saidawa.
A yayin bincike John ya tabbatar wa hukumar "yan sanda cewa ya dade yana wannan harkar kusan shekaru 17 da suka wuce amma ba'a sami nasarar capke shi ba sai a wannan karon.
No comments:
Post a Comment