Saturday, 23 September 2017

IRAN TAYI GWAJIN AKAMI MAI LINZAMI

IRAN TAYI GWAJIN AKAMI MAI LINZAMI
Duk da gaegadin da shugaban kasan Amurka, Mista Donald Trump yake yi wa kasar Iran kan ci gaba da kirkiran makamin mai linzami, yau Iran tayi gwanjin wani babban makami mai linzami. Wannan makamin da aka gwada gudunsa yau an tabbabtar zaiyi cimma nisan kilomita dubu biyu daga wurin da aka harba shi.
A ran sha tara ga wannan wata na satumba, Dunald Trump ya zargi kasan Iran a matsayin kasa mai goyon bayan ta’addanci da ‘yan ta’adda. Kuma ya kara da cewa mulkin da akeyi a Iran irin mulkin zalunci ne da babakere. Dunald Trump yayi wannan jawabin ne a gaban shuwagabannin duniya a taron majalisan dinkin duniya ta saba’in da dori.

A cewar sa, shugaban kasan Iran din, Rauhani, kasar sa bazata daina keram makamin mai hadari ba don suna son habaka karfin sun a soji. Kuma Rauhani ya mida martini wa Donald Trump a taron majalisar dinkin duniya cewa Dunald Trump ba komai bane in banda jahili, marar wayo kuma mai nuna kiyayyarsa a fili. 

No comments:

Post a Comment

An yanke hukuncin kisa Akan mutane buyer; Ko me dalili?

Kotu ta yanke hukuncin kisa Akan was mutane biyar a dalilin kashe wani makiyayi da sukayi.  Abin ya faru ne a kauyen Kadamun da ke karamar h...