Thursday, 21 September 2017

Ali Madu Sharif Yakai ziyara wa Osinbajo.

A yaune tsohon gwamnan Jihar Borno, Alhaji Ali Madu Sharif yakai ziyara wa mataimakin shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo. Jim kadan bayan fara ganawar tasu, shugaban Jam'iyya mai mulki; APC, Mista John Odigie Oyegun ya shiga wajen ganawar.
Ali Madu Sharif ya kadance tsohon dan Jami'iyyar APC ne kafin ya sauya sheka zuwa PDP. A kwanan kwanan nan, ya kasance shugaban babban Jam'iyyar adawa wato PDP ta kasa bayan tasha kaye a hanun APC.

A watan shekaran jiya ne, Kotu ta kwace shugabancin jam'iyar daga hanunsa ta bawa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmad Makarfi.

To ko shin da alamun Ali Madu Sharif zai sake sheka ne; ungulu ta koma gidanta na tsamiya? To saidai a saka ido a gani.

No comments:

Post a Comment

An yanke hukuncin kisa Akan mutane buyer; Ko me dalili?

Kotu ta yanke hukuncin kisa Akan was mutane biyar a dalilin kashe wani makiyayi da sukayi.  Abin ya faru ne a kauyen Kadamun da ke karamar h...