Sananne mai fada aji na jam'iyar mai mulki, APC, Alhaji Sami Ibrahim Daura, ya gargadi Sanata Shehu Sani Da Sanata Humkuyi game da Mal. Nasir Ahmad el-Rufa'i. Ya gargadi Sanatocin ne akan cewa su kyale mai girma Gwamna don ya sami sararin cigaba da ayyukan da ya fara wa al'ummar Jahar Kaduna. Yayi wannan gargadin ne a dakin manema labarai a babban birnin Jahar Kaduna.
Ya kara da cewa bai dace ba ga Sanatocin su ci gaba da cin dunduniyar gwamnan alhali dukanninsu yan jam'iyya guna ce. Yace idan Sanatocin suna da wata boyayyar matsala da Gwamna, bai kamata su dinga fitowa bainan jama'a suna fada dashi ba; ya dace su same shi a kebance su tattauna.
Bugu da kari, Sani Daura, ya karyata batun cewa Gwamna bai jin shawara. Yace babu mahalukin da baya jin shawara a duniyan nan.
No comments:
Post a Comment