A lokacin da wasu "yan kasa ke cecekuce kan rashin lafiyan shugaban kasa, uwar gidan shugaba Muhammadu Buhari ta koma kasar biritaniya wajen mai gidanta. Ganin cewa a "yan kwanakin nan maganganu sun yawaita a kan dawowar shugaban; ko zai dawo bada jimawa ba ko kuma sai ya kara lokuta don kara murmurewa. Wasu yan kasan na cewa lokacin dawowar tane yayi kusa shiyasa ta tafi don rako angonta gida Najeriya.
Jim kadan da tafiyar tane aka sami wasu yan kasa suke zanga zangar ko shugaba ya dawo ko ya sauka a mulkin kasan. Bugu da kari wasu, rahotanni sun karyata wasu makaryata kamar su Femi Kayode da Fayoshe cewa shugaba ba'a Landan yake ba ko Kuma ma baya raye.
No comments:
Post a Comment