RIGIMAR EL-RUFA'I DA HUNKUYI DA APC AKIDA KASUWAR BUKATA CE.
Daga Taskar Umar Kwangila
Tabbas, ba su na fada saboda Talaka ba ne, saboda duk ta'addancin da Gwamnatin Jahar Kaduna ke yi wa Talakawa na rushe-rushe da sauran su ba Mu taba jin inda Hunkuyi ya fito ya kalubalanci wannan Gwamnati Yar Jari Hujja ba. Hasalima, biyayya ya ke mata irin wacce bai taba yi wa wata Gwamnati a baya ba, kuma ya amfana tunda Gwamnatin Jahar Kaduna ta ba shi Commissioner da Interim Chairman don haka dole masu hankali su tambayi kan su dalilin da ya sa Hunkuyi ke ihu yanzu.
Tun farkon wannan Gwamnati ya kamata Hunkuyi ya mata bore bisa cin zarafin al'ummar da su ka kafa ta irin su Hon. Isah Ashiru Kudan da Dr. Hakim Baba Ahmad da sauran jiga-jigan da su ka taimaka wurin kafa ta, amma tunda an ba shi kason sa kowa ma ya mutu kawai. To, ba wai ina sukar Hunkuyi ba ne sai dai ina tuna mai abin da ya manta ne, kuma idan har za'a cigaba da gallazawa Talakawa ba Kai magana ba sai da aka zo kan ka, to ba amfani.
Sannan ina kira Mutane da su gane wannan fadan fa ba ana yi don cigaban Ku ba ne sai dai su na yi don cigaban su ne. Su na fadan handama da babakere ne akan delegates din da za su zabe su. Wadannan Mutanen su na fada da Gwamna ne, saboda ya yi Mu su CINYE DUKA DAN MUSA, kuma sun fahimci idan aka tafi a haka kashin su ya bushe idan 2019 ta shigo. Ya kamata Mutane su gane wadannan Mutanen fa duk takarar Gwamna su ke son yi, don haka idan ba su samu delegates ba kwabar su za tai ruwa.
Bayan haka, ya na da kyau Talakawa su gane Gwamna ba ya na fada da su ba ne sai dai ya yi abin da ya ke ganin zai kare mai mutumci ne. Gwamna ya shiga Daki daga shi sai wadansu tsiraru sun rubuta sunayen wadanda su ke so ne, saboda sune za su taimake shi a zaben ciro na 2019. Gwamna ya ware Hunkuyi ne, saboda ya na da Dan takara a Zone 1, kuma ya na tsoron kar ya ba shi damar da shi ma zai ce zai zo ya nemi Gwamna a 2019. Gwamna ya fahimci idan an yi free and fair election na delegates, to da yiwuwar ya sauka a Daudawa 2019 ba tare da kwari ba.
Don haka, wannan nada zare da ake yi ba don ni da kai ba ne, saboda wallahi ba Wanda za su taimaka a cikin Mu, kuma suna yi ne don biyan bukatar su a 2019. Da wannan na ke cewa idan ba'a yi wasa ba an zo gabar da APC a Jahar Kaduna za ta watse, saboda Gwamna ba zai taba canza list din da ya yi ba tunda ya ja ganin yin hakan abin kunya ne a gare shi tunda ana mai kirari da KAI KADAI GAYYA.
A karshe ina mai tabbatar maku da bayan tiya akwai wata caca, saboda a kalla Mutane Hudu ne da ke tafiyar a yanzu da su ka hada karfi da karfe don murkushe Nasiru a 2019, kuma ko wannen su kujerar Gwamna ya ke hari. To, ko da sunyi nasarar kwace delegates a hannun Gwamna kamar yadda su ke hari ina mai tabbatar maku da bayan tiya akwai wata caca. Don haka wannan fada ba don Talakawa ake yi ba KASUWAR BUKATA ce aka bude, kuma idan an bi daga-daga na kurya ka sha kashi.
No comments:
Post a Comment