*WASU DALILAI DA SUKE RAUNATA JIGON AUREN BAHAUSHE.*
*JAMIL NAFSEEN*
RASHIN IYA SOYAYYAR BAHAUSHE.
Rayuwar auren bahaushe kaso mai yawa tana tafiya ne kamar tafiyar gajiyayyar tsohuwa, a fara da marmari kafin a yi nisa an jigata sai gundira.
Na tattaro wasu dalilai dana gani, da kuma na sani... Yawanci bamu san ginshikan dake rike auren cikin farin ciki ba, abinda kawai muke rububin sani shine *kwanciya* da *rainon yara* da *zaman hakuri* har mu mace.
Dalilai na sune
*yawancin maaurata basa iya zaman tattaunawa dan farin ciki, sai dan wata matsalar dole
*mace bata iya yiwa mijinta kwalliya da tarairaya sai zata fita unguwa
*miji yakan ba matarsa abinci a baki ne kawai idan bata da lafiyar da ko abincin ba zata iya ci ba
*idan kaga miji ya budewa matarsa kofar mota in xasu fita to tabbata kofar nada matsala baiso ta kara lalacewa
*dalilin dake sa miji ya shafi wuyan matarsa kawai sai in tana zazzabi, zai taba yaji yanayin jikin, baxai sake tavawa ba sai wani zaxzabin.
*lokacin da miji xai dauki matarsa a kafada lokaci daya ne, idan tana nakuda.
*hakanan ba zaka ga mace ta siyawa mijinta kyauta ba ko ta tambaye shi me zaici? sai in yana asibiti a kwance.
*karka ga maaurata na zaune a kofar daki su biyu da daddare ka dauka suna hirar soyayya ne, suna jiran warin maganin sauron da suka sa ne a dakin ya gushe su koma ciki.
*ba zaka tava ganin miji da mata suna tsere ba sai lokacin da suke gujewa wata matsala kowa na neman ceton kansa.
*in miji da mata kaga sun iya wanka tare to sunyi lattin zuwa gun aiki ne kowa baiso ya kara makara
*lokacin da zaka ga mata tana kallon cikin idon mijinta da kulawa to datti ya fada idon ya nemi ta duba masa.
ta yaya aure da zamantakewa zata yi kargo a haka? Bayan ansan kyauta yaba tukuici ce, duk soyayyar data rasa armashin kulawa, tarairaya da lokaci raunata take.
Shuka tana yaduwa tayi kyau ne da taimakon ruwa da taki. Me yasa zamantakewar auren mu yake a sake sakaka kamar bata bukatar ruwa da taki ba?
Jamil nafseen
28/07/2017
No comments:
Post a Comment