Friday, 10 November 2017

RAYUWAR MATASA``` *AYMI NIGERIA* _KASHI NA HUDU_ BY..... ```COMRADE ABDUL KATSINA NATIONAL P.R.O I```

```RAYUWAR MATASA```
           *AYMI NIGERIA*
          _KASHI NA HUDU_
BY.....
```COMRADE ABDUL KATSINA NATIONAL P.R.O I```

Ko shakka babu, wannan abin shiri ne mummuna akanmu, mun sani ko bamu sani ba, mun yarda ko bamu yarda ba. Yanzu muna cikin karni na 21 wanda ana yakar mutane ba ta hanyar amfani da makamai ba. Ai mun sani ingila da ta so karya chaina, ai ba makami suka dauka suka far musu ba, a’a kwayoyi da wiwi suka shuka a kasar indiya kuma sukai chaina da su, kafin sinawa su farga tuni an jefa musu matasa cikin harkar shaye shaye.

A duk inda aka samu shaye shaye to al’umma ta kare, domin hankali yayi bankwana da wajen. To lokaci yayi da zamu dawo cikin hayyacinmu, mu nutsu musan cewar, anyi mana wuju wuju, tilas mu dawo mu nemi ina gabas take. Idan kuma ba haka ba, to mu sani harkar shaye shayen nan, abin ya wuce duk inda ake tsammani, domin maza nayi mata nayi, yara nayi manya nayi.

Idan muka yi shakulatun bangaro muna ji muna gani za’a rusa mu har kasa ba mu da wani katabus. Gwamnatocin Arewa da Sarakunan Arewa da kungiyoyin matasa da na dalibai da na Musulmai a Arewa lallai dole mu tashi mu yi yaƙi da batun shaye shayen matasa maza da mata, domin abin ya shafemu ta kusa ko ta nesa. Allah yasa mu farga.......
               *JOIN AYMI NIGERIA!!!*
*TOGETHER IN DEVELOP AREWA YOUTH*
                  *P. T. O*

No comments:

Post a Comment

An yanke hukuncin kisa Akan mutane buyer; Ko me dalili?

Kotu ta yanke hukuncin kisa Akan was mutane biyar a dalilin kashe wani makiyayi da sukayi.  Abin ya faru ne a kauyen Kadamun da ke karamar h...