IDAN BAKI YASAN ABINDA ZAI FITAR BAISAN ABINDA ZAI DAWO MASA NA MARTANI BA.
Martanin Wasu Kalaman Batanci da Gwomnan Jihar Kaduna Nasiru Elrufa'i Yayi wa Jam'iyar da Tayi Masa Riga da Wando Har da Babbar Riga a Najeriya Wato Jam'iyar PDP.
Martanin ya Fito ne Daga Bakin Maigirma Shugaban Jam'iyar PDP na Jihar Kaduna *Mr Hassan Hyet.*
Maigirma Mr Hassan Hyet ya Mayar da Martanin ne Kamar Haka.
Ina Mamakin Gwomna Nasiru Elrufa'i, Kulli Yaumin Bashida Wani Magana Gameda Jam'iyar PDP Idan ya Gaiyaci Kafafen Watsa Labarai, Sai Zagi Tareda Cin Mutuncin Jam'iyar PDP Damu Yayan ta Baki Daya.
Mr Hassan Hyet ya Cigaba da Cewa, Kamar Yanda na Sani Shima Nasiru Elrufa'i Yasan Haka, a Jihar Kaduna Kaf Babu Wani Dan Jam'iyar PDP Daya Amfana da Jam'iyar Kamar Shi Nasiru Elrufa'i.
Domin Kuwa ya Kasance Member a Jam'iyar na Tsawon Shekaru 13, ya Zama Chairman na BPE, ya Zama Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Dik a Karkashin Ita Jam'iyar PDP da Yake Zagi.
Kafin Zuwan Gwomnatin PDP Nasiru Elrufa'i ba Kowa Bane a Najeriya, Bashida Daki ko Guda Daya a Babban Birnin Tarayya Abuja, Balantana Yakai ga Mallakar Gidan Kansa.
Kafin Gwomnatin PDP ta Suturta Nasiru Elrufa'i, Shi Mutum ne Wanda Bashi da Wani Aikin yi Sai Yawo Daga Wannan Office Zuwa Wancen Office Neman Abin yi Shi Yasan Haka.
Wajan Maida Wannan Martani Maigirma Chairman ya Fusata Kwarai da Gaske, Inda ya Kira Gwomna Nasiru Elrufa'i da Kare, Kare Mara Amfani Wanda ko Mafarauta ba Zasuyi Tafiyar Farauta Dashi ba Sai Cikin Rashin Sani.
Ya Cigaba da Cewa Dik Abinda Gwomna Nasiru Elrufa'i Zaice Gameda Jam'iyar PDP, Shure Shure Yake Wanda Masu Hikimar Magana Suka Kira Bata Hana Mutuwa, Domin Yasan Cewa Taliyar Karshe Yake ci a Jihar Kaduna, ba Makawa Sai Yabar Kujeran da Yake Tinkaho da Ita 2019 da Yardan Allah.
Maigirma Mr Hassan Hyet ya Cigaba da Cewa, Bana Kokonto ko Kadan Nasiru Elrufa'i Karshensa a Gidan Yari Zata zo Masa, Saboda Irin Gagarumin Badakalar Daya Tafka Tareda da Wa'inda ya Bada Dama Ake Tafka wa a Karkashin Gwomnatinsa.
Ya Dibi Makudan Kudaden Jihar Kaduna ya Baiwa Dansa na Cikinsa, da Sunan Kwangilan Gyaran Kaduna State House of Assembly, ya Rarraba Kadarorin Jihar Kaduna Mallakar Jihar ga Yan'uwansa da Abokansa.
Ya Dibi Makudan Kudaden Jihar Kaduna ya Saye party excos Dinsa, Tareda Daukan Nauyinshu Zuwa Aikin Haji Dik da kudaden Jihar Kaduna, Dik Munsan Irin Wa'innan Badakalar da Gwomna Nasiru Elrufa'i ke Tafka wa a Wannan Jiha Tamu Kaduna.
Karo na Biyu a Maida Wannan Martani Maigirma Chairman Mr Hassan Hyet ya Fusata, Gameda Cin Mutuncin Jam'iyar PDP da Yayan ta da Gwomna Nasiru Elrufa'i Yake yi a Kafafen Watsa Labarai.
Inda ya Baiyana Gwomna Nasiru Elrufa'i Amatsayin Wani Annoba, Wanda Babu Wanda Zai so ya Kusanceshi Sai Cikin Rashin Sani ko Rashin Mafita ko Wata Jarabta ta Allah.
Mr Hassan Hyet Yace Dik Irin Abinda Shugaba Muhammadu Buhari Yayi wa Gwomna Nasiru Elrufa'i na Alkairi, Amma Kullum Bashida Wani Fata Irin ya Wayi Gari Yaji Ance Shugaba Muhammadu Buhari Baya Raye, Saboda ya Sami Damar Darewa Matsayin Mataimakin Shugaban Kasa.
Ubangiji ya Kunyatashi ta Hanyar Baiwa Shugaba Muhammadu Buhari Lafiya, Sai Muka Wayi Gari a Jihar Kaduna Gwomna Nasiru Elrufa'i Yana Abinda Masu Hikimar Magana ke Kira, Tabarmar Kunya da Hauka Ake Nadeta.
Inda ya Fasa Lalitar Gwomnatin Jihar Kaduna ya Dibo Makudan Kudade ya Gaiyaci Mawaka da Makida Maza da Mata, Suka Bazama Kan Tituna Suna Tika Rawa, Wai da Sunan Murnar Dawowar Shugaba Muhammadu Buhari.
Amma Kuma ya Kasa Zuwa Abuja Tarban Shugaba Buharin Lokacin da Jirginsa ya Sauka a Filin Jirgin Sama na Abuja.
Maigirma Mr Hassan Hyet ya Cigaba da Cewa, Abinda Gwomna Nasiru Yakamata ya Maida Hankali Akai Shine.
Cika Alkawuran Daya Dauka wa Al'ummar Jihar Kaduna, Tareda Magance Gagarumar Rikicin Daya Haddasa a Jam'iyar su ta APC a Jihar Kaduna, Amma ba Maida Hankali Wajan Zagi da Cin Mutuncin Jam'iyar PDP Tare Damu Yayan ta ba.
A Tarihin Jihar Kaduna Ba'a Taba Gwomna Mara Amfani Irin Gwomna Nasiru Elrufa'i, Domin Bashi da Aiki Sai Karya da Yaudaran Al'ummar Jihar Kaduna, Tareda Amfani da Karfin Mulki Wajan Cin Mutuncin Masu Mutunci.
Yaki Bari Ayi Zaben Kananan Hukumomi a Wannan Jiha Tamu, ya Karkatar da Makudan Kudaden da Za'ayi Amfani Dasu Wajan Shirya Zaben da Gudanar da Zaben.
A Karshe Maigirma Shugaban Jam'iyar PDP na Jihar Kaduna Mr Hassan Hyet Yace.
Mu ba Zamu Zagi Wani ko Muci Mutuncinsa ko Kuma mu Umurci Magoya Bayan Jam'iyar mu Suci Mutuncin Wani ba.
Amma ba Zamu Lamunci Wani Yaci Mutuncin mu Tareda Magoya Bayan Jam'iyar mu, Musamman Wanda Jam'iyar Tamu Tayi Tayi Masa Sha Tara ta Arziki ba Zamu Lamunci Wannan ba.
*WANNAN GASKIYA NE MY CHAIRMAN.*
Siyasa ba Hauka Bace mu Yakamata mu Dinga Fadin Abinda Muka Gadama Akan Gwomna Nasiru Elrufa'i, Saboda Jam'iyar mu ta PDP Tayi Masa Dikkanin Abinda Iyaye Zasu Iya Yiwa Dansu na Kyautatawa.
Amma Saboda Butulci Bayan ya Fice Daga Cikin ta, ya Maida Zagi da Cin Mutuncin jam'iyyar Tare Damu Yayan ta Abin yi, a Dik Lokacin da Zai Zanta da Kafafen Watsa Labarai.
Idan Mun Fusata Mun Mayar Masa da Martani Sai Ace Mana Marasa Da'a Mun Zagi Shugaba, Bayan Shi Shugaban Dik Sanda Zaiyi Magana Game Damu Banda Zagi da Cin Mutunci, Babu Abin Dake Fitowa Daga Bakinsa Gameda Damu.
To Enough is enough Inji Turawa Dik Sanda Nasiru Elrufa'i Yaci Mana Mutunci a Kafar Watsa Labarai, Babu Shakka ba Zamuyi Kasa a Gwuiwa ba Wajan Mayar Masa da Martanin Data Dace da Kalaman Daya Furta Game Damu da Jam'iyar mu ta PDP.
Domin Munada Abin Fada Game Dashi Fiye da Tinaninsa, Idan ya Manta ya Sani Shekaru 13 Yayi Acikin Gidan Jam'iyar mu ta PDP, Munada Record Dinsa Kaf, Wa'inda ya Sani Har ma da Wa'inda Bai Sani ba.
Idan Kunni Yaji............ Kuma da Yardan Allah Nasiru Elrufa'i Kaci Taliyar Karshe a Jihar Kaduna 2019 you must go Insha Allah.
No comments:
Post a Comment