Allah mai iko. Sugaban masu rajin kafa kasar BIAFRA, Namdi Kanu ya salwance. A halin da yanzu ake ciki, Namdi Kanu da manyan makarraban sa sun sun bar kayansu; sun noke a inda ba Wanda yasan yadda suke. A hira da manema labarai sukayi da kanin sa, yace "koni bansan yadda yayana ya salwance ba"
Amma abinda yafi bada mutane mamaki shine Oga Namdi Kanu yasha cika bakin cewa suna cikin shirin narkar da Najeriya da duk abinda take gadara dashi na dukiya da karfin soji. Ya sha alwashin shirin da yake dashi a halin yanzu ba irin ta Ojukwo bane Wanda tuni ya shafa wa gashin kansa ruwan sanyi kafin ya bar duniya.
Shidai mai gida Namdi Kanu, a cewarsa yana da hukumar sa da kayan yakin da ka iya yakar kasa kamar Najeriya ba tare da shan wahala ba.
A halin yanzu dai Namdi Kanu da Mahaifin sa, wanda yake sarkin kauyensu ne, a neme su an rasa. Hakan ne yasa nake tunawa da wata Karin magana da take cewa MAGANIN SHEGE SAI DAN BANZA. wato Magani KANU Sai sojin Najeriya.
To Allah ya sauwaqa mana fitina.
No comments:
Post a Comment