YADDA SHAN MIYAGUN KWAYOYI YAYI TASIRI A ZUKATAN MATASA
by...
```Comrade Abdul katsina```
Hakika matashi shine yake zama kashin bayan ko wacce al-umma ako wacce nahiya, rayuwar matashi idan ta gyaru babu shakka za asamu natsatstsar al-umma daga inda rayuwar matashi ta gurbace babu shakka rayuwar al-ummar da zata taso bayansa zata kasance lalataciyya,
A kasata najeriya musanman yankina na arewa Allah ya azurtamu da matasa ingantattu sai dai kash!!! Shan miyagun kwayoyi yayi tasiri a zukatansu wanda hakan barazana ce ga rayuwarmu ta da ya'yanmu
A birane da garuruwa da kauyuka da dama shaye-shayen kayan maye ya zama ruwan dare musamman a tsakanin mata,
Abin takaicin shi ne yadda muke kin mayar da
hankalin kan batun,
A matsayinmu na matasa mun fi mayar da hankali wajen yanke wa masu yi hukunci fiye da nemar musu mafita.
A yanzu haka muna asarar yan'uwa matasa musanman mata da yawa wadanda a maimakon su zama masu amfani da za a yi alfahari da su sai su rikidewa su zama 'yan kwaya.
Me yasa matasa da dama ke kara zama 'yan maye?
Me yasa suka mayar da shan kayan maye wasu abubuwan warkar musu da matsalolinsu?
Abin takaicin shi ne
yadda matasa suke kara dulmiyewa amma babu mai yin wani hobbasa cikin al'umma don dakatar da hakan,
Yara maza da mata kan fara shan kayen maye tun suna shekara 12 amma ba a farga da hakan sai lokaciya kure.
Iyaye ba su cika yarda cewa 'ya'yansu na wannan halayya ba, shugabannin al'umma kuma sunyi shiru.
Yaushe muka mayar
da dabi'ar shan kayan maye ta zama kamar ba
laifi ba a al'ummarmu?
Domin gano matsalolin tare da magance su kasance cikin masu bada gudunmuwarka a cikin kungiyar....
*AREWA YOUTH MOBILIZATION*
*INITIATIVE NIGERIA*
_(AYMI NIG)_
For more information
+234 806 650 3554 or
+234 808 789 2982
No comments:
Post a Comment