Shugaban masu fafutukan neman yankin Biafara, Namdi Kanu, yayi ikirarin cewa ba wanda zai iya zuwa ya kama shi a yankin Biafara kuma ya fita da rai. A cewar sa sakon neman yankin Biafara sako ne daga sama. A ranar lahadi, shugaban yayi ikirarin cewa bazai taba yiyuwa ayi zabe a jihar Abia ba sai an saurari kudurin su na basu yankin su.
" Ku sanar da Buhari, ina nan garin Aba kuma ina tabbatar muku duk wanda ya kuskura yazo kamani, to bazai bar nan a raye ba, kuma bazan taba guduwa in bar kasata ba". Inji Kanu.
Ya kara da cewa, "wasu jahilai suna kokarin kamani, to ni ina nan a Aba, kuma duk wanda yazo kamani bazai iya barin kasata ba, idan kuma wani yazo ya fita kalau, to nan ba kasar Biafara bane".
"Na gaya muku, babu zaben da zai yiwu a Anambra, fakat".
No comments:
Post a Comment