Friday, 14 July 2017

ME YASA AKA ZAFAFA HARIN BOMB A JAMI'AR MAIDUGURI? Daga Datti Assalafiy

ME YASA AKA ZAFAFA HARIN BOMB A JAMI'AR MAIDUGURI?

Daga Datti Assalafiy

Basu samun nasaran tayar da bamabamai a cikin jami'ar Maiduguri lokacin da muke karkashin  gwamnatin Jonathan irin na yanzu ba, kuma a lokacin ne Boko Haram sukaci karensu babu babbaka, amma mai yasa yanzu da muke karkashin gwamnatin Buhari ake samun nasaran tayar da bamabamai a jami'ar Maiduguri?

Ko dai don saboda a lokacin Jonathan kungiyoyin da ba na gwamnati ba (NGOs) basu mamaye jihar Borno kamar yadda sukeyi yanzu ba?

Burinsu shine a nakasa arewa ta bangaren ilmi, zasu cigaba da tayar da bomb a cikin jami'ar Maiduguri kamar yadda 'yan Bokoo Haram suka tabbatar, kunga daga karshe dole za'ace a rufe jami'ar

Daga nan kuma zasu nufi jihohin da suke makwabta da jihar Borno sucigaba da tayar da bomb a cikin jami'o'i wanda zaisa daga karshe a kulle makarantun, an raunata arewa ta wannan fannin, domin hankalinsu ya tashi ganin yadda matasan arewa suke tururuwan shiga jami'a don neman ilmin boko

Ance babban coordinator na kungiyoyin NGOs dake fadin jihar Borno ya karbi hayar wani daki a hotel a Maiduguri, a kullun zai biya kudin haya dubu goma (10,000), ya karbi hayar dakin na tsawon shekara goma (10) kuma ya biya kudin, wanda ya kama kimanin naira miliyan talatin da shida (36,000,000) don Allah wannan kudin bai kai su gina gida ba amma suka karbi haya? Me zasuyi a cikin dakin?

Boko Haram sun fitar da wani faifan video kwanannan, bayan mai jawabi yana jawabi a cikin videon, sai kuma akaji muryan wani mutumi irin wanda suke tallen magani a kasuwa da lasifika yana tashi, wanda hakan yasa aka fahimci cewa videon anyishi ne a cikin gari kuma a boye a cikin daki, anya ba irin dakin da NGOs suka karbi haya bane kuwa?

Kwanaki mun  mun bayyana muku cewa mun fahimci Boko Haram suna da wani boyayyen masana'antar kera bamabamai a cikin garin Maiduguri, yanzu da muke bincike kuma muke fahimtar manufofin kungiyoyin NGOs, anya  ba daya daga cikin gidajen da 'yan NGOs suka karbi haya a Maiduguri Boko Haram suke kera bamabaman ba kuwa?

Kullun NGOs sai kara mamayar garin Maiduguri suke, gaskiya bamu yarda dasu ba, shugabannin arewa wadanda hakkin tsaron rayukanmu ya rataya a wuyansu don Allah susa ayi bincike domin daukar matakin gaggawa

Muna rokon Allah Ya tona asirin makiyanmu

No comments:

Post a Comment

An yanke hukuncin kisa Akan mutane buyer; Ko me dalili?

Kotu ta yanke hukuncin kisa Akan was mutane biyar a dalilin kashe wani makiyayi da sukayi.  Abin ya faru ne a kauyen Kadamun da ke karamar h...