Monday, 31 July 2017

"YAN IS BIYU SUN KAI HARI OFFISHIN JAKADANCIN IRAQI

"Yan ta'addan kungiyar ISIS 4 sun kai wani mumunan hari a ofishin Jakadancin Iraqi da ke garin Kabul, babban birnin Afghanistan. Harin ya aukune a safiyar yau litinin yanda wani dan kunan nakin wake ya tada bam da ke daure a jikin sa sai kuma wasu mutane uku suka bude wa masu gadin offishin jakadancin na Iraqi.

Mai magana da yawun Ministan cikin gida, Najib Danish yace ma'aikatan ofishin biyu ne yan Afghanistan suka rasa rayuwar su a harin sannan an raunana "yan sanda uku.

A cewar su, kungiyar ta IS, tace mayakan ta sunyi nasarar halaka mutane bakawai ne ba biyu ba duk da cewa su kungiyar sun saba ruruta barnar su suna wuce gona da iri. Bugu da kari, kungiyar ta karyata cewa maharar su ba guda hudu ne suka kai hari ba; su biyu ne kacal suka yi wannan barnar.

Shugaban kasan ta Afghanistan, Ashraf Gani, yayi Allah wadai da hadari kuma yace hakkin gwamnati ne su bada kariya ga hukumomin kasan waje.

No comments:

Post a Comment

An yanke hukuncin kisa Akan mutane buyer; Ko me dalili?

Kotu ta yanke hukuncin kisa Akan was mutane biyar a dalilin kashe wani makiyayi da sukayi.  Abin ya faru ne a kauyen Kadamun da ke karamar h...