Sunday, 6 August 2017

Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Gargadi Iyaye Masu Tura Yaransu Mata Hannun Boko Haram- Daga Habu Dan Sarki

Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Gargadi Iyaye Masu Tura Yaransu Mata Hannun Boko Haram

Daga Habu Dan Sarki

Rundunar sojojin Nijeriya ta yi kira ga iyaye, malaman addini da shugabannin al'umma, musamman wadanda ke yankin Arewa maso Gabas, da su guji bayar da yaran su mata suna taimakawa 'yan ta'addan Boko Haram wajen tayar da bama bamai da wanke musu kwakwalwa, ana cusa musu tsattsauran ra'ayin addini.

A wata takardar sanarwa da ta fito daga kakakin rundunar sojojin Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, an bayyana cewa, an gano wannan danyen aiki da wasu iyaye ke aikatawa ne bayan wasu tambayoyi da aka yi wa wasu yara mata da aka kama suna kokarin tayar da bama bamai na kunar bakin wake.

A binciken da aka gudanar a cewar sanarwar an gano yadda wadannan baragurbin iyaye ko masu riko ke jefa rayuwar yaransu cikin halaka, a maimakon dora su a hanyar da ta dace da yi musu tarbiyya ta gari.

Don haka rundunar na kara kira ga jama'a su yi hattara kuma su taimaka wajen kawo karshen wannan dabbanci da ta'addanci da yake cigaba da gudana a Arewa maso Gabas, tare da kai rahoton duk wani uba ko iyayen da suke ba da sadakar yaransu mata ga 'yan Boko Haram, ko kuma inda aka ji rahoton bacewar wasu 'yan mata.

Domin isar da sakon gaggawa ga rundunar sojojin Nijeriya za a iya kiran wannan lamba 193 da kowanne layin waya. Akwai tukwicin naira dubu 500 da aka tanada ga duk wanda ya tseguntawa jami'an tsaro yadda za a gano masu dasa bam a cikin jama'a.

©Zuma Times Hausa

No comments:

Post a Comment

An yanke hukuncin kisa Akan mutane buyer; Ko me dalili?

Kotu ta yanke hukuncin kisa Akan was mutane biyar a dalilin kashe wani makiyayi da sukayi.  Abin ya faru ne a kauyen Kadamun da ke karamar h...